Wasu manyan kungiyoyi biyu sun yi kira ga majalisar dokokin kasar nan da ta janye shirin yin amfani da sama da dala miliyan 56 don siya wa ‘yan majalisar dokokin da wasu jami’ai motocin alfarma guda 465 masu kariyar harsashi.
Shugabannin kungiyar sa ido a kan harkokin da suka shafi majalisun dokoki ta CISLAC da kungiyar SERAP mai sa ido kan tattalin arzikin al’umma a Najeriya, sun ce wannan kudurin tamkar nuna halin ko in kula ne ga yanayin kuncin da talakawan Najeriya ke ciki.
Kungiyar SERAP ta kuma ba hukumomin wa’adin mako guda su yi watsi da shirin.
Kungiyoyin biyu sun kira ga masu goyon bayan shirin marasa kishin kasa musamman a daidai lokacin da ake fuskantar tashin farashin man fetur, da hauhawar farashin abinci da sauran kayayyakin masarufi.