• Home  
  • Mutane uku sun mutu a rikicin manoma da makiyaya a Jigawa
- Labarai

Mutane uku sun mutu a rikicin manoma da makiyaya a Jigawa

Rundunar ƴansandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum uku tare da jikkata biyu a wani rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a jihar. Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Lawan Shiisu Adam ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru en a ƙauyen Malamawar Fulani da ke yankin ƙaramar hukumar Garki. Ya ce […]

Rundunar ƴansandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutum uku tare da jikkata biyu a wani rikici da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a jihar.

Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Lawan Shiisu Adam ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru en a ƙauyen Malamawar Fulani da ke yankin ƙaramar hukumar Garki.

Ya ce lamarin ya faru ne bayan da aka zargi wasu makiyaya da shigar da dabbobi gonakin manoma domin, abin da ya sa manoman da mutanen ƙauyen suka mayar da martani ta hanyar yunƙurin korarsu.

”Sakamakon hakan ne aka samu arangama tsakanin ɓangarorin biyu, lamarin da ya haddasa rasuwar mutum uku da raunata biyu,” in ji shi.

SP Shiisu ya ce zuwa yanzu hankula sun kwanta a yankin, an ci gaba da gudanar da al’amura.

”Kuma muna ci gaba da gudanar da bincike domin kama waɗanda ke da hannu a tashin fitinitar”, in ji kakakin ƴansandan.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai