Akalla mutum biyu ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya auku da tawagar Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari.
Hatsarin ya faru ne a daren ranar Juma’a a kusa da wani kauye mai suna Jimkamshi, yayin da gwamnan da tawagarsa ke hanyar zuwa Kafur, mahaifiyarsa domin jefa kuri’a a zaben gwamna da na ‘yan majalisun jihohi da ake gudanarwa a yau.
Majiyarmu ta rawaito cewa wadanda suka mutu a hatsarin sun hada da ‘yansanda guda biyu a tawagar gwamnan masu suna Kabir Adamu da Nura Safiyanu, yayin da wasu kuma suka gamu da raunuka amma suna kan samun kulawar Likitoci a asibiti.
Kodayake har zuwa lokacin da wakilinmu ke aiko da rahoton gwamnati jihar ba ta fitar da wani bayani a kan wannan hatsarin ba.