A karon farko tun bayan da ya fara magana kan matsalar tsaro a Najeriya, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya amince cewa ana kashe Musulmai a ƙasar.
A baya, Trump ya sha bayyana cewa hare-haren da ake kai wa a Najeriya sun fi shafar Kiristoci kaɗai, duk da cewa rahotannin sun nuna cewar mutane daga kowane addini na fuskantar hare-haren ta’addanci.
A wata hira da ya yi da jaridar New York Times, Trump ya ce tashe-tashen hankula ba iya addini ɗaya suke shafa ba.
Lokacin da aka tambaye shi game da bayanin da mai ba shi shawara kan harkokin Afirka ya yi cewa Boko Haram sun fi kashe Musulmai sama da Kiristoci, Trump ya kafe kan matsayarsa.
A ƙarshen watan Oktoba, Trump ya fara gargaɗin cewa Kiristanci na fuskantar barazana a Najeriya.
- Ƙungiyar matasan ƙabilar Ijaw ta buƙaci Tinubu ya sauke Wike
- Dangote ya kai ƙarar tsohon shugaban NMDPRA zuwa EFCC
Ya kuma yi barazanar ɗaukar matakin soji a kan ƙasar, inda ya zargi gwamnatin Najeriya da gazawa wajen daƙile hare-haren da ake kai wa Kiristoci.
Daga bisani, Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashe masu “matsala ta musamman”.
Sai dai Gwamnatin Tarayya ta tura wata tawaga zuwa Amurka domin bayyana wa hukumomin ƙasar halin da ake ciki game da matsalar tsaro a Najeriya.
Bayan wannan ziyara, manyan jami’an gwamnatin Amurka, sun ziyarci Najeriya domin samun bayanai kai-tsaye kan halin tsaron ƙasar.
