Ƙungiyar Likitoci Masu Sanin Makamar Aiki ta Najeriya (NARD), reshen Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zariya, ta sanar da aniyarta ta shiga yajin aiki na ƙasa da aka shirya fara wa a ranar 12 ga watan Janairu, 2027.
Wannan ya biyo bayan gazawar Gwamnatin Tarayya wajen cika yarjejeniyar da ta cimma da ƙungiyar.
Shugaban ƙungiyar, Dokta Haruna-Saleh Usman ne, ya bayyana hakan ta bakin Mataimakin Shugaban ƙungiyar, Dokta Yusuf Ibrahim, yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Zariya a ranar Juma’a.
Dokta Ibrahim ya ce, baya ga ajiye aiki, reshen ABUTH zai kuma gudanar da zanga-zangar lumana a harabar asibitin.
Ya bayyana cewa sun yanke wannan matsaya ne bayan taron majalisar ƙungiyar, inda mambobinta suka amince baki ɗaya da tsunduma yajin aikin.
A cewarsa, taron manema labaran na da nufin sake jaddada buƙatun ƙungiyar, duk da sanya hannu kan yarjejeniya tsakanin NARD da Gwamnatin Tarayya.
Ya ƙara da cewa NARD ta shiga yajin aikin da aka yi a faɗin Najeriya a ranar 1 ga watan Nuwamban 2025, bayan doguwar tattaunawa, wadda ta kai ga sanya hannu kan yarjejeniya a ranar 29 ga watan Nuwamba, 2025.
Dokta Ibrahim ya ce yarjejeniyar ta ƙunshi buƙatu 19 da suka shafi walwalar ma’aikata, albashi da ci gaban ƙwarewar likitoci da ke koyon aiki a faɗin ƙasar.
- Na Gamsu Ana Kashe Musulmai A Najeriya — Trump
- Ƙungiyar matasan ƙabilar Ijaw ta buƙaci Tinubu ya sauke Wike
Ya ce daga cikin muhimman abubuwan da aka amince da su, kuma aka tanadi mako biyu domin aiwatarwa, akwai dawo da likitoci da ke koyon aiki da aka sallama daga Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Lokoja, a Jihar Kogi.
“Abin takaici, har yanzu ba a mayar da su bakin aikinsu ba. Maimakon haka, gwamnati na ƙoƙarin tura su wasu asibitoci, abin da ya saɓa da yarjejeniyar da aka yi,” in ji shi.
Ya bayyana cewa yawancin likitocin da abin ya shafa sun riga sun yi nisa a koyon aiki kuma sun kusa rubuta jarabawa, inda ya ce tura su wani waje zai tilasta musu fara ɗaukar horo daga farko.
“Mun ɗauki wannan a matsayin zalunci kuma abin da ba za mu amince da shi ba,” in ji shi.
Haka kuma, Dokta Ibrahim ya nuna damuwa kan jinkirin tura bayanan ƙarin girma da ake bin likitoci da ke koyon aiki a wasu cibiyoyi zuwa Ofishin Kasafi da Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya domin a biya su.
Ya ƙara da cewa har yanzu ba a aiwatar da cikakken jadawalin alawus da aka amince da shi ba, ciki har da bashin baya, kuma ba a saka shi a cikin kasafin kuɗin ƙasa na shekarar 2026 ba.
Ƙungiyar ta kuma bayyana damuwa kan rashin fayyace batun tsallake matsayi da daidaita matsayin shiga aiki, inda ta yi kira ga Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da ta fitar da bayyanan umarni ga shugabannin cibiyoyin lafiya da sauran masu ruwa da tsaki.
