Shugaban Majalisar wakilan Najeriya, Tajuddeen Abbas ya yi kira ga al’ummar ƙasar dasu kwantar da hankulansu tare da tsayar da zanga-zangar da suke yi,inda ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki na tattaunawa kan shawo kan matsalolin ƙasar.
Shugaban Majalisar wakilan ya yi wannan kira ne kwana ɗaya bayan matasan ƙasar sun shiga zanga-zangar nuna fushin su kan matsin rayuwa da ake ciki.
A tattaunawarsa da mane ma labarai, Abbas ya ce ya gana da matasa inda ya ji koken su, kuma tuni ya sanar da shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Najeriya dai na fama da matsalar tashin farashin kayan masarufi da zubewar darajar Naira.
Wanda hakan ya haifar da matsin rayuwa ga ‘yan kasar musamman kananan ma’aikata da ‘yan kasuwa.
Matasan ƙasar dai sun ayyana zasu yi kwanaki goma suna gudanar da zanga-zanga, wadda aka fara a jiya Alhamis.