Home » Zanga-zangar Lumana Ta Yi Ajalin Mutane 14 A Najeriya

Zanga-zangar Lumana Ta Yi Ajalin Mutane 14 A Najeriya

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya ta rikide zuwa tashin hankali, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 14 a manyan biranen kasar. 

Zanga-zangar dai ta samo asali ne sakamakon cire tallafin man fetur da kuma karyewar darajar Naira.

Zangar-zangar da a farko aka tsara a matsayin ta lumana ta janyo asarar rayuka 14, ta kuma kawo cikas ga harkokin kasuwanci, lafiya da ilimi.

A babban birnin tarayya Abuja, an yi arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro, inda harsashi ya kashe wani matashi a mahadar NNPC da ke Kubwa, kuma ana zargin jami’an tsaro da harbe matashin.

A jihar Kano, cibiyar kasuwancin  Najeriya, an tabbatar da mutuwar wani matashi a yayin zanga-zangar da aka yi a Unguwar Hotoro, karamar hukumar Tarauni. 

A halin da ake ciki, akwai wani mutum guda a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ya ji mummunan rauni sanadiyyar harsashi da ya same shi yayin zanga-zanga a Jihar Kano.

A jiya Alhamis 1 ga Agusta, a jihar Kano an kama sama da mutane 200 da laifin fasa shagunan mutane da niyyar sace kayayyakin da ke ciki. 

Yayin da tuni hukumomi suka tabbatar da cewa an kwashe kayan aiki da aka zuba a sabon ofishin NCC da ke jihar Kano, an kuma tabbatar da cewa masu zanga-zanga sun lalata kayayyakin gwamnatin Jihar da na manyan ‘yan kasuwar jihar.

A jihar Kebbi, rahotanni na tabbatar da cewa an kashe mutum daya a garin Yauri a lokacin da yake kokarin kulle shagonsa  bayan wasu masu zanga-zanga na shirin wawushe masa kayansa. 

Yayinda ake juyayin mutuwar mutane a  Abuja da Kano da Kebbi, rahotanni daga jihar Kaduna na cewa an kashe masu zanga-zanga biyu, an ce an kashe daya daga cikin masu zanga-zangar ne a kusa da gidan gwamnatin jihar.

Kawo yanzu dai hukumomin tsaro a jihohin Najeriya na ci gaba da bayyana rashin jin dadinsu biyo bayan yadda masu zanga-zangar ke afka musu a lokacin da suke kokarin basu kariya. 

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?