A yayin da aka shiga wuni na uku da fara zanga-zangar tsadar rayuwa a fadin ƙasa, an samu hatsaniya a tsakanin wasu matasa da jami’an tsaro a kan sabon titin Mandawari dake birnin Kano.
Tuni dai zanga-zangar ta rikide zuwa tashin hankali inda ta haifar da sanya dokar hana fita da har yanzu ake zaune cikin yanayi na zullumi.
A cewar shaidun gani da ido, matasan sun fito titin ne domin shaƙatawa, inda su kuma jami’an ‘yan sandan yankin da sojojin da ke sintiri suka buƙaci su koma gida, amma hakan ba ta samu ba.
- Na Isar Da Koken Ku, Ku Hakura Da Zanga-zanga-Tajudden Abbas
- Zanga-zangar Lumana Ta Yi Ajalin Mutane 14 A Najeriya
Wannan turjiya da matasan suka yi wa jami’an tsaron ne ya sa ka harba borkonon tsohuwa domin tarwatsa su.
Abokin aikinmu Hassan Abdu Mai Bulawus ya yi iya kokarinsa domin jin ta bakin mai Magana da Yawun ‘Yan Sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, amma haƙarmu ba ta cim ma ruwa ba.