Tsohon Babban Hafsan Sojojin Sama na Najeriya kuma tsohon ɗan takarar Gwamnan jihar Bauchi a Jam’iyyar APC a zaben 2023, Iya Marshal Sadique Baba Abubakar (mai ritaya), ya ce ya yi ritaya daga harkokin siyasa saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba.
Ɗaya saga cikin fitattun magoya bayansa, Huzaifa Yari, ya tabbatar wa manema labarai cewa wannan batu.
Sadique ya shiga siyasa ne a shekarar 2021 bayan ya yi ritaya daga aikin soji, ina ta fito a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu takarar Gwamna Bauchi a zaɓen 2023, amma Gwamna Bala Mohammed na jam’iyyar PDP ya kayar da shi.
Amma duk da haka, a wani mataki da ya ba magoya bayansa da abokan hamayyarsa da dama mamaki, ya sanar da barinsa harkokin siyasa baki ɗaya.
A cikin wani gajeren sakon bidiyo da aka fitar ga mutanen Jihar Bauchi cikin Harshen Hausa a ranar Asabar, Saddique ya bayyana wannan mataki a matsayin mai wahala kuma ya nemi afuwa ga magoya bayansa.
Duk da cewa ya janye daga siyasa, ya ce zai ci gaba da bayar da gudummawa ga ci gaban Jihar Bauchi da kuma taimakawa al’umma, musamman a fannin lafiya da ilimi ta hanyar “Gidauniyarsa Kula da ’Yan Adam ta Marshal.”
“A yau, da zuciya mai cike da baƙin ciki, na yanke shawara mai wahala ta barin harkokin siyasa baki ɗaya,saboda dalilai na ƙashin kaina.
“Wannan shawara ba ta zo da sauƙi ba, idan aka yi la’akari da ƙauna, goyon baya, da kuma ƙaunar da mutanen Jihar Bauchi da ’yan Najeriya suka nuna mini tun lokacin da na shiga siyasa a 2021.”
Ya nuna godiya ga magoya bayansa kuma ya yi addu’ar Allah Ya albarkace su.
“Ina ba da haƙuri ga dukkan magoya bayana da masu yi mini fatan alheri kan wannan shawara mai wahala, kuma ina yi wa kowa fatan alheri,” in ji shi.
Saddique ya ƙara tabbatar da cewa ritayarsa daga siyasa ba za ta hana shi yi wa ɗan adam hidima ba.
“Ficewa daga siyasa ba zai hana ni ci gaba da tallafawa al’umma ta hanyar Gidauniyar Kula da Marshal ba, musamman a fannonin ilimi da kiwon lafiya,” in ji shi.
Ya kammala jawabinsa da addu’ar fatan zaman lafiya, kwanciyar hankali, da ci-gaban Jihar Bauchi da ƙasa baki ɗaya.
