• Home  
  • Najeriya na ƙara sa ido bayan ɓarkewar Ebola a Congo
- Babban Labari

Najeriya na ƙara sa ido bayan ɓarkewar Ebola a Congo

Hukumar Daƙile Yaɗuwar Cututtuka a Najeriya, NCDC ta ce duk da cewa ba a samu ɓullar cutar Ebola ba a ƙasar, tana ƙarfafa matakai don sa ido sakamakon mutuwar mutum 88 a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo da kuma samun mutum guda da aka bayar da rahoton ya kamu da cutar a Uganda. Cikin wata sanarwa da […]

Hukumar Daƙile Yaɗuwar Cututtuka a Najeriya, NCDC ta ce duk da cewa ba a samu ɓullar cutar Ebola ba a ƙasar, tana ƙarfafa matakai don sa ido sakamakon mutuwar mutum 88 a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo da kuma samun mutum guda da aka bayar da rahoton ya kamu da cutar a Uganda.

Cikin wata sanarwa da Darakta Janar na hukumar, Jide Idris ya fitar a ranar Lahadi, hukumar NCDC tana shirya ayyukan wayar da kai da kuma a faɗin ƙasar.

Matakin na zuwa ne yayin da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ayyana ɓarkewar Ebola a Congo da Uganda a matsayin babban abin damuwa.

Hukumomin lafiya ta ce ɓarkewar cutar tana ɗauke da babban haɗari saboda tuni aka gano ƙwayar cutar a Uganda sannan kuma an samu mutanen da suka kamu a Kinshasa da ke Congo.

Cutar da ta fara ɓulla a Lardin Ituri na Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo ta shafi kusan mutum 246.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000