Wani ɗan takarar sanata na shiyyar Yamma na jihar Nassarawa Wakili Kabiru-Muhammad, ya shigar da ƙara gaban wata kotu saboda cire tambarin jam’iyyarsa ta NNPP da hukumar zaɓen ta yi a zaɓen da aka gudanar a ranar 25 ga watan da ya gabata.
A yayin da yake magana da manema labarai bayan shigar da ƙara da ya yi a yau a garin Lafiya, ya bayyana cewa hukumar zaɓe ba ta saka tambarin jam’iyyar tasa ba akan takardar kaɗa ƙuri’a.
Inda Kanfanin Dillancin Labarai ta ƙasa NAN ya rawaito cewa wannan ƙara ta shafi hukumar zaɓe mai zaman kanta ne da kuma ɗan takarar jam’iyyar SDP wanda aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen da aka yi a watan da ya gabata.
Mai ƙarar dai na buƙatar kotu da ta soke zaɓen da aka yi tare da yin kira ga magoya bayansa da su yi haƙuri kuma su rungumi zaman lafiya da kuma shirin sake kaɗa masa ƙuri’a.