Hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kano, ta mayar da martini kan zargin da ake yi musu cewar, basa kama manyan dilolin miyagun kwayoyi sai iya suke siya don sha suke kamawa.
jami’in hulda da jama’a na hukumar reshen jihar Kano, ASN Sadik Muhammad Maigatari, ne ya musanta zargin, inda ya ce basa barin duk wanda aka samu da laifin ta’ammali da miyagun kwayoyi domin aikin hukumarsu shi ne kama masu siyarwa da kuma masu sha.
Maigatari ya kara da cewa , miyagun kwayoyin da ake ta’ammali da su, duk shigo da su ake yi , kuma suna daukar matakan dakilewa ta hanyar sanya shingayen bincike a hanyoyin shigowa jihar.
Haka zalika ya ce sanya shingayen binken ya taikama mu su sosai, wajen kama miyagun kwayoyi masu yawa ciki harda kwayoyin Tiramadol, Akuskura da tabar Wiwi wadanda za su illata tarbiyar al’umma.
- Matsalar tsaro: Gwamnatin Yobe ta rufe duk makarantun sakandaren kwana
- Yau Atiku zai karɓi katin zama ɗan a Jama’iyyar ADC
NDLEA ta ce suna yin aiki da dukkan sauran hukumomin tsaro kuma duk wanda aka kama da kayan maye ana gurfanar da shi agaban kotu bayan kammala bincike.
A karshe ya ce sabon kwamandan hukumar ya kara karfafa wa dakarun da suke shingayen binciken gwiwa don ci gaba da samun nasarar dakile shigo da kayan mayen jihar Kano.
