• Home  
  • Nijar ta zargi Faransa ta kitsa juyin mulki a ƙasar
- Kasashen Ketare

Nijar ta zargi Faransa ta kitsa juyin mulki a ƙasar

Hukumomin Nijar sun zargi Faransa a hukumance da goyon bayan abin da suka bayyana a matsayin “yunkurin kawo hargitsa ƙasar a ranakun 28 da 29 ga watan Agusta.” A cikin wata sanarwa, gwamnatin Nijar ta ce arangamar da ta faru a sansanin sojin sama na 101 da ke Yamai, tana da “alaƙa da ƙasashen duniya”, […]

Hukumomin Nijar sun zargi Faransa a hukumance da goyon bayan abin da suka bayyana a matsayin “yunkurin kawo hargitsa ƙasar a ranakun 28 da 29 ga watan Agusta.”

A cikin wata sanarwa, gwamnatin Nijar ta ce arangamar da ta faru a sansanin sojin sama na 101 da ke Yamai, tana da “alaƙa da ƙasashen duniya”, tana mai cewa “an tattara ƙwararan shaidu masu yawa dangane da hari, kuma ana tunanin kai ƙarar gaban kotunan ƙasa da ƙasa.”

Sanarwar ta kuma ce “Shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ke jagorantar wata babbar kafa ta mutane da ƙungiyoyi da ke goyon bayan wannan aiki,” yayin da ta kuma yi zargin cewa wasu ƙasashen Afirka da ba a bayyana sunayensu ba sun taka rawa a matsayin masu shiga tsakani.

Sai dai zuwa yanzu, gwamnatin Nijar ba ta gabatar da wata shaida da za ta tabbatar da waɗannan zarge-zarge ba.

Sansanin sojin sama na 101, wanda aka kai wa hari a ranar 29 ga watan Agusta, wani ɓangare ne na rukunin filin jirgin saman Diori Hamani. A wurin ne ake ajiye jiragen yaƙin sojin Nijar da jirage marasa matuƙa, tare da wata rundunar yaƙi da ta’addanci ta ƙawancen ƙasashen Sahel.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, sojojin Rasha da na Italiya ma suna da sansani a wurin.

Nijar ta ce baya ga Rasha, ta kuma samu taimako daga Aljeriya.

Rasha ta tabbatar da cewa dakarunta sun taimaka wajen dakile abin da aka bayyana a matsayin yunkurin juyin mulki da aka yi ranar Asabar a Nijar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000