• Home  
  • Amurka za ta sayar wa Saudiyya makamai na dala biliyan 5
- Kasashen Ketare

Amurka za ta sayar wa Saudiyya makamai na dala biliyan 5

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da amincewa da wata yarjejeniya ta sayar wa Saudiyya kayan makamai da darajarsu ta kai dala biliyan 5. A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce ta amince da buƙatar Saudiyya na sayen dubban bama-bamai da kuma na’urorin jagorantar makamai masu linzami masu dogon zango. A cewar […]

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da amincewa da wata yarjejeniya ta sayar wa Saudiyya kayan makamai da darajarsu ta kai dala biliyan 5.

A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce ta amince da buƙatar Saudiyya na sayen dubban bama-bamai da kuma na’urorin jagorantar makamai masu linzami masu dogon zango.

A cewar ma’aikatar, ban da makaman, yarjejeniyar za ta haɗa da manyan makamai da kayayyakin gyara da sinadarai da kuma ayyukan tallafin fasaha da dabarun sufuri da samar da kayayyaki.

Amurka ta bayyana yarjejeniyar a matsayin wani mataki na inganta tsaron wata muhimmiyar ƙawarta, tare da taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiyar siyasa da ci gaban tattalin arziki a yankin Tekun Fasha.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa yarjejeniyar za ta taimaka wajen ƙarfafa ƙarfin tsaron sararin samaniyar Saudiyya domin fuskantar barazanar da ake samu a yankin a halin yanzu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai