Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya sanar da komawa aikin neman mai a yankin Tafkin Chadi da ke jihar Borno.
Kamfanin ya dakatar da aikin ne a watan Yuli na shekara ta 2017, bayan da wasu mahara da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka kai wa ma’aikatan hari har suka yi garkuwa da wasu.
Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabi ta intanet ga taron kaddamar da komawa kan aikin gano man a wata rijiya da ke yankin Wadi-B a garin Tuba na karamar hukumar Jere.
Kamfanin ya ce yana da kyakkyawan zato cewa za a samu mai da gas mai yawan gaske a wannan wuri.