Jam’iyyar NNPP ta yi Alla-wadai da kalaman kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Ibrahim Waiya, wanda ya buƙaci mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo ya ajiye aikinsa.
Wata sanarwa da kakakin jam’iyyar a jihar Kano, Ibrahim Karaye ya fitar, ya ce har yanzu kundin tsarin mulki ya bai wa mataimakin gwamnan ci gaba da riƙe mukaminsa.
Kalaman kwamishinan yaɗa labaran na zuwa ne bayan da mataimakin gwamnan ya ki bin gwamna Abba Kabir Yusuf tare da wasu muƙarrabai sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, inda NNPPn ta ce Abdussalam na da ikon ci gaba da gudanar da ayyukansa saboda sun yi takara tare gwamnan jihar.
Jam’iyyar ta buƙaci ɓangaren zartaswa a jihar da ya daina shiga al’amuran siyasa, ya tsaya kan ayyukan da kundin mulki ya ba shi damar aiwatarwa.
“Ci gaba da aikin mataimaikin gwamna yana da muhimmanci wajen ɗorewar shugabanci a jihar Kano,” in ji sanarwar NNPP.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa kwamishinan yaɗa labaran ba ya nan lokacin da ake gwagwarmayar kafa gwamnati, don haka ya ja bakinsa ya yi shiru.

