Tag: NNPP

Babban Labari

Mataimakin Gwamnan Kano Ya Yi Murabus

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo ya yi murabus daga muƙaminsa. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar Kwankwasiyya ta fitar, wadda kakakinta Dr Habibu Sale Mohammed ya fitar da yammacin ranar Juma’a. Ya ce mataimakin gwamnan ya ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano da tabbatar […]

Babban Labari Labarai

NNPP ta yi watsi da shirin Amurka na ƙaƙaba wa Kwankwaso takunkumi

Jam’iyyar NNPP ta yi watsi da ƙudirin da wasu ’yan majalisar dokokin Amurka suka gabatar na sanya jagoranta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, cikin jerin waɗanda za a ƙaƙaba wa takunkumi. Wasu ’yan majalisar Amurka sun gabatar da ƙudirin neman hana Kwankwaso biza tare da ƙwace kadarorinsa, bisa zargin sa da hannu wajen take ’yancin addini. […]

Babban Labari Labarai

Ba mu da shirin sauke Sarki Sanusi II — Gwamnatin Kano

Gwamnatin Kano ta yi fatali da jita-jitar da ake yaɗawa kan cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga kan mulki bayan sauya sheƙar gwamnan daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC mai mulki. Gwamnan ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da Aminiya kan lamarin […]

Babban Labari Siyasa

NNPP ta soki masu kiran cewa mataimakin gwamnan Kano ya ajiye aiki

Jam’iyyar NNPP ta yi Alla-wadai da kalaman kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Ibrahim Waiya, wanda ya buƙaci mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo ya ajiye aikinsa. Wata sanarwa da kakakin jam’iyyar a jihar Kano, Ibrahim Karaye ya fitar, ya ce har yanzu kundin tsarin mulki ya bai wa mataimakin gwamnan ci gaba da riƙe […]

Babban Labari Siyasa

Kwankwaso ya karyata rahotan Premium Times na cewa ya goyi bayan gwamnan Kano zuwa APC

Jagoran jam’iyyar NNPP, Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso, ya musanta wani rahoto na jaridar Premium Times da ke cewa ya goyi bayan shirin sauya sheƙar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC. Wannan na cikin sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Hon. Saifullahi Hassan, ya fitar a ranar Talata. Sanarwar ta ce […]

Babban Labari Siyasa

An jibge motocin yaƙi a Gidan Gwamnatin Kano

An tsaurara ƙarin jami’an tsaro a gidan Gwamnatin Jihar Kano a safiyar Litinin a yayin da ake dakon sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf. Wakilinmu ya lura cewa an girke ƙarin ’yan sanda da jami’an hukumar tsaro ta DSS a babbar ƙofar shiga da wasu muhimman wurare a gidan gwamnatin. Sojoji sun ceto fasinjojin da […]

Babban Labari Siyasa

2027: Jam’iyyar NNPP ta rantsar da sabbin shugabanni a Gombe

Jam’iyyar NNPP ta rantsar da sabbin shugabanninta a Jihar Gombe, inda ta jaddada muhimmancin haɗin kai da farfado da jam’iyyar tun daga matakin ƙananan hukumomi zuwa jiha gabanin zaɓen 2027. Taron ya halarta bayan zuwan wakilai daga dukkanin ƙananan hukumomin jihar. Mambobin jam’iyyar sun yaba da yadda komai ya gudana cikin lumana da tsari, abin […]

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai