Gwamnatin tarayya ta Amince da tsarin Shirya kaso 70 na fina-finan Katun ga Yara daga gida Nijeriya.

 

Gwamnatin Nijeriya ta amince da wani sabon tsari wanda zai tabbatar da ana shirya kaso 70 cinkin 100 na fina-finan wasan yara wato Katun, a wani yunkuri na chusa kishin kasa a zukatan yara.

Shugaban hukumar NOA na kasa Mallam Lanre Issa-Onilu, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da kwamitin mutane bakwai tare da hadin gwiwar hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa NBC.

Mallam Lanre ya ce hakan zai taimaka wajen koyawa yara al’adun gida Nijeriya da Sanya kyawawan dabi’u a zukatan yan kasar.

Majalissar zartarwa ta kasa ce, ta amince da kaso 70 na fina-finanKatun din da ake haskawa a gidajen Telebijin da aka shirya su a gida Nijeriya ba daga kasashen ketare ba.

Ya kara da cewa shirye-shiryen Katun suna da tasiri sosai wajen nunawa Yara kyawawan dabi’u da kuma kishin kasa, inda ya bayar da misalin cewa a shekarun da suka gabata kafafen yada labaran kasar sunfi Sanya wadanda aka shirya daga ketare.

Ya kuma ce yin hakan zai sanya kishin kasa da da’a da kuma yin aiki tukuru wanda zai samar da hadin kai mai dorewa.

Mallam Lanre, ya tabatar da cewa samar da katun , a gida zai zai samar da zaman lafiya da hadin kai da mutunta al’adu wanda zai sanya wa yaran kwarin gwiwar bayar da gudunmawa.

Daraktar kula da tsare-tsare ta hukumar kafafen yada labarai NBC, Mrs Stella Erhunmwunsee,ta ce hukumar zata sake inganta dokokin kafafen yada labarai , musamman shirye-shiryen katun da aka samar a Nijeriya, inda ta yi alkawarin yin aiki tare da kafafen yada labarai don wayar da kai da kuma bayar da horo.

Mambobin kwamitin sun haɗa da, Alhaji Nunu Kobi NOA, Mallam Bala Musa NOA, Barista Williams Dogo NOA, Mrs Blessing Oyem NOA, Mrs Sharifat Adegbesan NOA, Mrs Stella Erhunmwunsee NBC , Susan Obi NBC da kuma Pauline Ehusani NBC.

Mallam Issa-Onilu, ya yi kira ga mambobin kwamitin da su yi aiki tukuru don cimma manufar da aka sa a gaba na ci gaban ƙasa da kuma al’adun ta.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *