Hukumar lafiya ta Duniya (WHO) ta ce kimanin mutane 922 ne aka bayyana cewa sun kamu da cutar kwalara ko amai da gudawa a Najeriya.
A yayin da mutane 32 suka mutu sakamon cutar a shakerar nan da muke ciki.
Cutar Kwalara ko amai da gudawa, cuta ce da ake kamuwa da ita sakamakon ɗaukar wata ƙwayar cuta da ake kamuwa da ita ta hanyar cin abinci ko shan ruwa gurɓatacce da ke ɗauke da ƙwayar cutar.
Cutar dai kan zo da tsanani wanda a wasu lokutan ma takan yi barazana ga rayuwar wanda ya kamu da ita, matuƙar bai samu kulawar gaggawa ba.
Ita ma a wani rahoto, Hukumar Daƙile Yaduwar Cututtuka ta Ƙasa ta wallafa wasu bayanai a shafinta na intanet da ke nuna cewa an tabbatar da samun mutane 157 da ke ɗauke da cutar sankarau tsakanin watan Oktoban bara zuwa watan Maris ɗin da muke ciki.
Haka kuma an samu marasa lafiya da ake zargin sun kamu da cutar su kusan 628, ciki har da mutane 52 da suka mutu a jihohin ƙasar nan 21.
Alamomin cutar sun haɗar da zazzaɓi da ciwon kai da tashin zuciya da amai, da sanƙarewar wuya da sauransu.
Muhasa Rediyo na shawartar al’umma da su ziyarci asibiti da zarar sun ji waɗannan alamomi.