Hukumar shirya jarrabawa ta WAEC ta zamanantar da tsarin fitar da sakamakon jarrabawar da take yi na kammala makarantar sakandire a faɗin Afirka.
A watanni biyar da suka wuce ne hukumar shirya jarrabawar ta sanar da daina amfani da takarda wajen bayar da sakamakon jarrabawa ga ɗalibai
Tun a shekarar 1999 ne hukumar ke amfani da takarda wajen ba wa ɗalibai sakamako wanda hukumar ta tabbatar zamanantar da tsarin nata.
A cewar hukumar, daga yanzu ɗalibai da hukumomi da ƙungiyoyi da ke son tabbatar da sahihancin sakamakon jarrabawa, to za su iya yin hakan ne kaɗai ta hanyar ziyartar shafinta na intanet.
Ta shafin intanet ɗin dai ɗalibai za su iya duba sakamakonsu, sauke sakamakonsu da kuma damar tura sakamakonsu na ainihi zuwa ga duk wanda suke so.
Shugaban Hukumar WAEC a Najeriya Patrick Areghan ya ce sabbin ɗalibai da tsofaffi za su iya amfani da shafin ne bayan sun biya naira 7,500,
Domin tura sahihin kwafin, wato original a Turance, ɗaliban za su biya naira 3,500, tare da biyan 5,000 domin tabbatar da sahihancin sakamako.