• Home  
  • Ribar da muke ci ta ragu da Naira biliyan 720 a watan Yuli – NNPCL
- Babban Labari - Labarai

Ribar da muke ci ta ragu da Naira biliyan 720 a watan Yuli – NNPCL

Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya ce ya tafka babbar asara inda ribar da ya ci ta Naira biliyan 905 a watan Yuni ta ragu zuwa Naira biliyan 185 a watan Yulin da ya gabata. Hakan dai na. nufin ribar kamfanin ta fadi da kimanin kaso 79.6 cikin 100. Kamfanin, a cikin rahotonsa na wata-wata […]

Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ya ce ya tafka babbar asara inda ribar da ya ci ta Naira biliyan 905 a watan Yuni ta ragu zuwa Naira biliyan 185 a watan Yulin da ya gabata.

Hakan dai na. nufin ribar kamfanin ta fadi da kimanin kaso 79.6 cikin 100.

Kamfanin, a cikin rahotonsa na wata-wata da ya fitar ranar Alhamis, ya ce ya yi jimillar cinikin Naira tiriliyan 4.41 a watan Yuli, sabanin na Naira tiriliyan 4.57 da ya yi a watan da ya gabace shi.

NNPCL ya kuma ce ribar da ya samu a watan Yuni ita ce biliyan 905, ta watan Mayu kuma tiriliyan 1.05, yayin da a watan Afrilu kuma ya ci ribar biliyan 962.

Alkaluman dai sun nuna ainihin faduwa a kudaden shigar kamfanin, duk kuwa da cewa adadin danyen man da kasar ke haka ya karu daga ganga miliyan 1.68 a kullum zuwa ganga miliyan 1.7.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000