Rikici na kara bazuwa a Jamhuriyar Kamaru kwana guda bayan Kotun Kolin ta tabbatar da Shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa mai cike da takaddama.
Dan takarar jam’iyyar adawa, Issa Tchiroma Bakary, ta sake bayyana cewa ba zai amince da sakamakon zaben ba, yana mai cewa “zaben ba sahihi ba ne” yana mai yin fatali da nasarar Shugaba Biya.
Sanarwar sakamkon ta janyo zanga-zanga, kone-kone da fada a tsakanin jama’a da jami’an tsaro a biranen Douala da Mbouda da Bertoua da Batouri, inda ake ci gaba da samun rikice-rikice lalata dukiyoyi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ana ci gaba da kona gine-gine da farfasa abubuwa, da satar kaya a wasu manyan birane ciki har da Douala Mbouda da Bertoua.
Bayanai sun nuna cewa ofishin ’yan sanda na tsakiya a Bertoua na cikin barazana, yayin da masu zanga-zanga suka mamaye tituna a Batouri da ke yankin gabas, lamarin da ya haddasa tashin hankali mai tsanani.
A yankunan Mbanga da Njombé da Souza, jita-jitar zuwan ’yan tawayen Ambazonian ta sanya malamai sun rufe makarantu, suka sallami ɗalibai gida, abin da ya ƙara haifar da fargaba da rudani a tsakanin al’umma.
- Majalissar Dattawan Nijeriya Zata Tantance Sabbin Hafsoshin Tsaro A Ranar Laraba
- NiMet Ta Yi Hasashen Samun Hazo A Wasu Jihohin Najeriya
Jami’an tsaro sun mayar da martani ta hanyar harbe-harbe da hayake mai sanya hawaye da kuma ruwan zafi, domin tarwatsa masu zanga-zanga, wadda aka fara cikin lumana, kafin ta rikide zuwa tarzoma a sassan ƙasar.
Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun kwato buhunan shinkafa da aka sata yayin tarzomar da ta faru a Douala.
Wani ɗan jarida ya bayyana cewa halin da ake ciki yana sauyawa , inda ake sa ran wasu yankuna za su iya shiga cikin hatsaniya nan gaba kadan.
A halin yanzu, ƙungiyar Amnesty International Africa ta roƙi hukumomin Kamaru su girmama haƙƙin jama’a na gudanar da zanga-zanga cikin lumana, tare da yin bincike mai zaman kansa cikin gaskiya kan mutuwar da aka samu a yayin tarzomar.
Haka kuma, rahotanni daga yankin Yamma, musamman a garin Bafoussam, sun nuna cewa ana jin sautin harbe-harbe da ke ƙara tayar da hankalin jama’a.
A Souza da Njombe na yankin Littoral, jama’a sun shiga rudani bayan jita-jitar cewa ’yan tawayen Ambazonia sun kutsa garuruwan, abin da ya sa iyaye suka yi tururuwa don kwashe ’ya’yansu daga makarantu.