Jagoran ‘yan adawa a Senegal, Ousmane Sonko ya buƙaci ‘yan kasa su fito kwansu da kwarkwata sun yi zanga-zangar adawa da manufar shugaba Macky Sall ta neman takara a karo na uku.
A yau Litinin ake sa ran shugaba Sall zai gabatar da jawabi domin sanar da anniyarsa ta takara a zaben 2024 ko akasin haka- matakin da akasari kwararu a fannin shari’a ke cewa zai karya ƙundin tsarin mulkin Senegal.
Mista Sanko ya ce ya shafe tsawon shekaru yana fuskantar barazana a rayuwarsa, saboda kwadayin mulki na mutum guda.
A watan da ya gabata, Dubban mutane suka fantsama kan tituna su na zanga-zanga a biranen Senegal bayan yanke hukunci shekaru biyu kan Mista Sonko akan ɓata matasa.
Magoya-bayan Mista Sonko da wasu masu sharhi na ganin wannan hukuncin ƙoƙari ne kawai na datse shi daga takarar shugaban kasa a zaben baɗi.