Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif, ya rushe shugabancin hukumar kare hakkin masu siyan kayayyaki ta Jihar wato (Consumer Protection Council) dukkan su saboda ricikin shugabanci .
Sakataren gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran sa ya fitar, inda ya ce matakin ya biyo bayan dogon rikicin shugabancin da ya dabaibaye hukumar, duk da kokarin da aka yi wajen tabbatar da zaman lafiya, a hukumar amma hakan bata samu ba.
A cewar, “Bisa umarnin gwamna Abba Kabir Yusif, Shugaban hukumar, da Sakataren Zartarwa da dukkan mambobi, ciki har da mambobin Ex-Officio, duk an rushe su nan take”.
- Rundunar Yan Sandan Kano Ta Kama Wasu Mutane Da Ake Zargin Yan Bindiga Ne A Shanono.
- Hisbah Zata Mikawa Kotu Batun Janye Auren Mai Wushirya Da Yar Guda.
Umar Faruk, ya kuma umarci dukkan jami’an da abin ya shafa su mika ragamar aiki tare da dukkan kayayyakin gwamnati da ke hannunsu ga jami’in da ya fi kowa matsayi a hukumar, a ranar Litinin, 27 ga watan Oktoban 2025.
A ƙarshe sanarwar ta ce gwamnatin Jihar Kano za ta ci gaba da daukar matakai don tabbatar da ingantaccen shugabanci, da gaskiya, da kyakkyawan shuganci a hukumominta.