Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito daga Mujallar Wall Street cewa ana sa ran Sakataren Rundunar Sojin Ƙasa ta Amurka, Dan Driscoll, zai yi murabus kafin ƙarshen shekara, bayan watanni ana samun takun-saka tsakaninsa da Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth.
Mujallar Wall Street Journal ta wallafa rahoton ne bisa bayanan wasu mutane da ke da masaniya kan dambarwar.
Sai dai Reuters ta ce har yanzu ba ta samu damar tabbatar da rahoton da kanta ba.
Idan aka tabbatar da murabus ɗin Driscoll, hakan zai sa Rundunar Sojin Ƙasa ta Amurka ta kasance ba tare da shugaba da Majalisar Dattijan Amurka ta tabbatar da nadinsa ba, a daidai lokacin da Washington ke ci gaba da yaƙi da ta ƙaddamar tare da Isra’ila kan Iran, wanda yanzu ya shafe kusan wata shida.
