Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta ƙirƙiro wani kwamiti da zai fito da hanyoyin da kowanne jami’in ɗan sanda zai mallaki muhalli ba tare da yasha wahala ba.
Muƙaddashin babban sufeton ƴan sanda Najeriya, DIG Sulaiman Muhammed Abdul, ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da dakarun ƴan sandan jihar Kano, a madadin shugaban ƴan sanda na ƙasa, IGP Olatunji Rilwan Disu, a ranar Laraba.
Ya ƙara da cewa a kwanakin da suka gabata an ƙarawa ƙananan ƴan sanda dubu 17 girma, kuma yanzu haka akwai muƙaddasan kwamishinonin ƴan sanda da za su samu ƙarin girma.
Haka kuma ya ce an ƙara inganta horas da dakarun rundunar musamman ta hanyar Internet da kuma fashaar zamani ta ( AI).
DIG Sulaiman Abdul, ya ƙara da cewa muƙasudin zuwansa Kano shi ne ya haɗa kan jahohin arewacin Nijeriya maso yamma, domin gano matsalalin tsaron yankin tare da ɗaukar matakan magance su.
Ya ɓukaci haɗin kan al’umma tare da kira ga ƴan jarida su dinga tuntuɓarsu kafin fitar da labarin da suka samu domin tabbatar da sahihancinsa.
A ƙarshe ya gargaɗi, jami’an ƴan sandan da su kasance masu bin doka da oda, da kuma ƙauce cin zalin jama’a.
