Rundunar yan sandan jihar Kano ta sanar da fara aiwatar da dokar hana amfani da motocin da ake rufe lambobinsu, da kuma wadanda ba su da lamba.
Kakakin rundunar yan sandan jihar , CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce matakin ya fara aiki nan take.
Sanarwar ta ce rufewa ko cire lambar mota na hana jami’an tsaro gano motocin da ake amfani da su wajen aikata laifuka kamar fashi da makami, garkuwa da mutane, da safarar miyagun kwayoyi.
Sanarwar ta ce za a kwace motocin da suka karya dokar tare da gurfanar da direbobinsu a gaban kotu.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bukaci masu ababen hawa su tabbatar da cewa motocinsu suna da ingantattun lambobin masu rajista a gaba da baya, tare da cire duk wani abin da ke hana ganin lambobin a fili.
Rundunar ta jaddada cewa ba a ɗauki matakin domin takura wa wasu ba, sai don inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano.
