Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta gana da ƙungiyoyin farar hula (CSOs) domin tattauna hanyoyin hana tashin hankali a lokutan zaɓe, a wani ɓangare na bikin ranar ƴan sandan Nijeriya ta shekarar 2026.
Sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa da wayar da kai kan illar tayar da hankalin al’umma a lokutan zabe, tare da ƙudirin tabbatar da zaman lafiya.
Masu ruwa da tsaki sun yaba da wannan yunƙuri tare da yin alƙawarin bada goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

