Rundunar sojin Najeriya ta gargaɗi mutanen da ke yin kira da a yi juyin mulki a ƙasar nan saboda tsadar rayuwa da ake ciki.
Wannan na zuwa ne a lokacin da ƙasar nan ke cigaba da fuskantar matsaloli da suka shafi tattalin arziƙi da tsaro waɗanda suka haifar da zanga-zanga a kwanakin baya a wasu jihohin ƙasar nan.
Yawancin wannan kiraye-kiraye dai an fi yin sa ne a dandalin shafukan sada zumunta inda har wasu ke kwatanta mulkin sojin Nijar a yanzu a matsayin cigaba ga ƙasar.
Wannan hali ya sa wasu daga cikin al’ummar ƙasar nan ke ganin idan al’amura suka ƙi saituwa a lokacin shugaba Tinubu, to kamatuwa ya yi sojoji su karɓi ƙasar nan domin dawo da ita kan turba.
Sai dai a lokacin da babban hafsan tsaron ƙasar nan, Janar Christopher Musa ke mayar da martani a yayin zantawarsa da manema labarai a wurin taron ƙaddamar da muhalin runduna shiyya ta shida a Fatakwal ta jihar Ribas, ya ce masu wancan kiraye-kiraye sam ba su da kishin ƙasar nan tare da yin gargaɗin cewa za a ɗauki mataki a kansu.
Hafsan sojojin ya ce rundunar tasu za ta cigaba da yin abin da ya kamata wajen kare dimokraɗiyyar ƙasar nan.
Duk da haka, ya yarda cewa al’umma na cikin wani mawuyacin hali, sai dai bai ga alfanun kiraye-kiraye na juyin mulki ba, saboda a ganinsa ƙasashe da ke kan doron dimokraɗiyya sun fi samun cigaba da sauri saɓanin mulkin soja.