Rundunar tsaron Najeriya ta ce akwai wasu marasa kishin kasa da ke Ingiza ta domin yi wa Shugaba Tinubu juyin mulki.
Rundunar ta bayyana haka ne ta bakin kakakinta, Birgediya Tukur Gusau, a yau.
Cikin sanarwar da ya aike wa manema labarai, inda ya bayyana cewa wasu marasa kishin ci gaban Najeriya ne ke ƙoƙarin shirya maƙarƙashiya.
Sai dai kakakin hukumar bai yi karin haske ko ya bayyana wadanda ake zargi da ingiza rundunar ba.
Ya ce babu wata zuga da za ta ingiza sojoji yin juyin mulki a Najeriya ganin yadda aka sha wahala kafin samun dawowar dimukradiyya a kasar nan.
Gusau ya ce tsarin dimukradiyya ya kawo ci gaba ga ƙasar nan, kuma za su yi watsi da duk wani tsari da zai kawo cikas ga dimokraɗiyya.
Ya kara da cewa, sojojin za su ci gaba da aikin kare kasar kamar yadda ya ke a kundin tsarin mulki madadin sauraron wasu gurbatattu daga kasar.
Wannan martani na zuwa ne bayan wasu na zuga sojoji domin ƙwace mulki daga farar hula ganin yadda suka shafe shekaru suna mulki ba tare da kawo karshen matsalolin kasar ba.
Gusau ya ce rundunar karkashin jagorancin babban hafsanta, Christopher Musa ba za su yi karan tsaye ga kundin tsarin mulkin kasar ba.