Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA, za ta ci gaba da kama yara masu tuƙa baburan a-daidaita-sahu waɗanda ba su kai shekara 18 ba.
Shugaban Hukumar KAROTA Injiniya Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka, a lokacin da yake karbar baƙuncin gamayyar ƙungiyoyin a-daidaita-sahu na jihar nan, a ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mansur Tanimu
Injiniya Faisal ya ce Hukumar KAROTA ba za ta amince da bai wa ƙananan yaran da ba su kai shekara 18 tuƙin a-daidaita-sahu ba.
Sannan, Hukumar ta ce ba za ta yarda da yin amfani da waya a lokacin tuƙi ba, da kuma ɗaukar kaya fiye da kima a cikin a-daidaita-sahu
Sai dai gamayyar wasu ƙungiyoyi a Kano sun roƙi gwamnatin jihar da ta samar da makarantar da za ta bayar da horo ga matuƙa a-daidaita- sahun faɗin jihar nan, domin hakan zai taimaka wajen rage aikata laifukan tuƙin da ake gani a kan titunan jihar nan.