• Home  
  • Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wadanda ake zargi da kashe matar aure da yayan ta 6 a Dorayi.
- Babban Labari - Labarai

Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wadanda ake zargi da kashe matar aure da yayan ta 6 a Dorayi.

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta samu nasarar kama mutanen da ake zargi da kashe matar aure da yayan 6, a unguwar Chiranchi Dorayi dake karamar hukumar Kumbotso. Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Lahadi. Sanarwar […]

Rundunar yan sandan jihar Kano, ta samu nasarar kama mutanen da ake zargi da kashe matar aure da yayan 6, a unguwar Chiranchi Dorayi dake karamar hukumar Kumbotso.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce wanda ake zargi da jagorantar kisan gillar mai suna Umar Auwalu, dan uwan marigayiyar ne, inda ya hada kai da abokansa da yanzu haka suke hannun yan sanda.

Wadanda ake zargin sun hada da Umar Auwalu mai Shekaru 23 mazaunin unguwar Sabuwar Gandu, Isiyaku Yakubu dan Shekaru 40 da ake Kira da Chebe mazaunin unguwar Sagagi da kuma Yakubu Abdul’aziz dan shekaru 21 da ake Kira da Wawo mazaunin unguwar Sabon gida Sharada dukka dake jihar Kano.

Binciken farko-farko da jami’an yan sanda suka gudanar wadanda ake zargin sun Amsa laifin da ake zargi su.

CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya kara da cewa an samu kayan wadanda ake zargin da jinin mamatan a jiki da kuma wayoyi da Kudi da suka yi Fashin su tare da Wata Gora da sauran muggan makamai.

A karshe rundunar yan sandan jihar Kano, ta ce yanzu haka bincike yana ci gaba da gudana kafin daukar mataki na gaba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai