• Home  
  • Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kammala tantance masu neman shiga aikin ɗan sanda
- Babban Labari

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta kammala tantance masu neman shiga aikin ɗan sanda

Rundunar  yan sandan jihar Kano ta kammala aikin tantance masu neman shiga aikin ƴan sanda cikin kwanciyar hankali da lumana a jiya Asabar, 18 ga watan Afrilu, 2026, wanda ya gudana a wajen shakatawa na manyan jami’an yan sanda Police Officers’ Mess dake Bompai. Aikin tantancewar wanda aka fara tun daga ranar 9 ga Maris […]

Rundunar  yan sandan jihar Kano ta kammala aikin tantance masu neman shiga aikin ƴan sanda cikin kwanciyar hankali da lumana a jiya Asabar, 18 ga watan Afrilu, 2026, wanda ya gudana a wajen shakatawa na manyan jami’an yan sanda Police Officers’ Mess dake Bompai.

Aikin tantancewar wanda aka fara tun daga ranar 9 ga Maris zuwa ranar 18 ga watan Afrilun 2026, ya kasance cikin tsari da bin ka’idojin rundunar ‘yan sanda da kuma hukumar kula da aiyukan yan sanda ta ƙasa PSC, inda aka yi gwajin jiki da kuma duba takardu.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya godewa mukaddashin kwamishinan DCP Habibu Rabiu, da jagoranci tantancewar.

Sanarwar ta fito ne ta bakin CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, jami’in Hulɗa da jama’a na Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano.

Kwamishinan yan sanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da yadda aka gudanar da aikin cikin gaskiya da bin doka, tare da gode wa dukkan masu ruwa da tsaki.

Ya kuma gargadi jama’a cewa aikin daukar ‘yan sanda kyauta ne, yana mai yin kira da a guji masu damfara.

An kammala aikin cikin tsaro ba tare da wata matsala ba, inda aka taya masu nema fatan samun nasara.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai