• Home  
  • Rundunar ƴan sandan Kano ta sha alwashin magance matsalolin tsaron yankin Ɗorayi da kewaye.
- Babban Labari

Rundunar ƴan sandan Kano ta sha alwashin magance matsalolin tsaron yankin Ɗorayi da kewaye.

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce za ta yi zama na musamman tare da masu ruwa da tsaki na Ɗorayi da kewaye, ta yadda za a lalubo hanyoyin magance matsalalolin tsaron da ke damun yankunan. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan a Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a […]

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce za ta yi zama na musamman tare da masu ruwa da tsaki na Ɗorayi da kewaye, ta yadda za a lalubo hanyoyin magance matsalalolin tsaron da ke damun yankunan.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan a Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a lokacin da gamayyar Kwamitocin tsaro na Ɗorayi da kewaye suka kai masa ziyara ta musamman, domin tattauna wa a kan yadda za a magance matsalolin tsaron yankunan.

CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya kuma ce, a shirye Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Ibrahim Adamu Bakori, yake wajen yin duk abinda ya kamata domin ganin an daƙile matsalolin tsaro a Ɗorayi da kewaye.

Ya kuma yabawa shugabannin gamayyar Kwamitocin tsaron na yankunan Ɗorayi da kewaye, kan irin ƙoƙarin da suke yi na bada gudunmawar su ga hukumomin tsaro, domin ganin an kawo ƙarshen matsalar tsaron da ke damun wasu sassan yankunan.

Da yake nasa jawabin, Shugaban Gamayyar Matasan Kano, kuma guda daga cikin shugabanni a Kwamititocin Ɗorayi da kewaye, Muhammad Tijjani Ɗorayi (MTD) ya ce sun kai ziyarar Hedikwatar rundunar sandan jihar Kano, ne, domin miƙa buƙatar su ga Kwamishina CP Ibrahim Adamu Bakori, don ganin an ƙara ƙarfafa tsaro a yankunan nasu.

A cewarsa, “Babban burin mu shi ne a kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin Ɗorayi da kewaye, da ma jihar Kano, baki ɗaya, tare da taimakon matasan yankin ta ɓangarori daban-daban,” in ji MTD.

A yayin ziyarar dai, shugabannin Kwamitocin tsaron na Ɗorayi da Kewaye, ƙarkashin jagorancin Mallam Abdullahi Idris Ɗan Fodiyo, da ma ne suka halarta, a ranar Juma’a 3 ya Yuni, 2026.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000