Daga Muazu Hardawa Edita jàridar
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haifar da ambaliyar ruwa wacce ta share babbar gadar garin Buskuri da ke karamar hukumar Katagum a Jihar Bauchi.
Ambaliyar ta jefa dubban mutane da gonakin su da gidaje cikin gagarumar asarar da bata misaltuwa.
Buskuri gari ne mai nisan kilomita 15 daga Azare zuwa Potiskum.
A halin yanzu, lamarin ya haifar da cikas ga dukkan masu bin hanyar da suka fito daga Kano zuwa Maiduguri.
Ta tilastawa matafiya canza hanya, yadda dole sai sun bi ta Azare su zagaya zuwa Misau su dawo Bulkachuwa kafin su dauki hanya zuwa Potiskum.
Malam Aminu Umar Minista Mai Unguwar Nassarawa a Buskuri ya bayyana wa wakilinmu Muazu Hardawa, Bauchi cewa tun da hantsi ruwan ya fara ambaliya a cikin garin na Buskuri.
Kawo yanzu rahotanni na cewa ruwan ya shanye garin, ya kuma rusa fiye da rabin gidajen garin ya haka Kuma ya lalata daruruwan gonakin hatsi da shinkafa da ridi da sauran kayan amfanin gonakin yankin.
Alhaji Aminu Umar ya bayyana cewa dattijai da ke garin sun bayyana cewa duk da cewa garin yana kusa da kogi amma sama da shekara 70 basu taba ganin irin wannan lamarin ba.
Ya Kara da cewa a wannan Alhamis ɗin ruwan ya fara tahowa ta kogin ya yanke gefe guda na gadar kafin daga baya ya share gadar baki ɗaya, inda aka daina bin hanyar aka zuba wa sarautar Allah ido.
Malam Aminu Umar ya roki hukumar agajin gaggawa ta kasa da gwamnatin Jihar Bauchi da kungiyoyi masu ba da agaji su kawo musu dauki don taimaka wa mutanen da suka tagayyara, saboda rushewar gidaje sun rasa kayan abinci da suka mallaka sun zamo labari.
A wannan Alhamis ɗin sun tsinci kan su a wani yanayi da basu taba zaton samun kan su a ciki ba.
Don haka ya Roki gwamna Bala Mohammed Abdulkadir na Jihar Bauchi ya taho Azare domin duba yadda barnar zanga zangar kuncin rayuwa ta kasance ya kamata ya karaso don gamewa idonsa irin mawuyacin halin da garin Buskuri ya abka cikin kankanen lokaci.
Tuni dai muka samu labarin gwamnatin Jihar Bauchi ta aika wata tawaga ta musamman don ganin halin da yankin ya shiga kafin gwamna Bala Mohammed ya isa don ganin yadda ambaliyar ruwan ta kasance.