Rahotanni daga hedikwatar Kungiyar kwadago ta Najeriya ta NLC na cewa gungun jami’an tsaro dauke da tarin makamai sun yi wa hedikwatarta da ke Abuja, kawanya.
NLC ta ce jami’an tsaro sun isa ginin hedikwatar ta su ne da ake kira Labour House.
Shugaban sashen hulda da jama’a na NLC Benson Upah ya ce jami’an sun karya kofar ma’ajiyar littattafai da ke hawa na biyu na ginin inda suka kwashe littattafai da takardu.
Benson Upah ya ce, jami’an sun ce suna neman wasu takardu da aka yi amfani da su yayin zanga-zanga a Najeriya.
NLC ta ce zuwa yanzu ba ta iya tantance abubuwan da jami’an tsaron suka kwashe ba, sai dai ta yi kira da a gaggauta janye jami’an daga hedikwatar ta su.