A jiya ne Dr. Olayemi Cardoso, ya kama aiki a matsayin shugaban riƙo na babban bankin Najeriya, CBN.
Wannan na ƙunshe ne cikin wani jawabi da daraktan Sadawar na babban bankin, Isa AbdulMumin, ya fitar, inda ya tabbatar da cewa Cardoso’s ya kama aiki a matsayin shugaban babban bankin Najeriya na riƙo har zuwa lokacin da Majalisa za ta tabbatar da shi a matsayin cikakken shugaba.
Wannan na zuwa ne bayan ajiye aiki da tsohon gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele, ya yi.
Su ma mataimakan gwamnan sun fara kama aiki na riƙo kafin tabbatar da su.
Tuni dai shugaban da mataimakansa suka karɓi rantsuwar kama aiki a yayin wani ɗan ƙwarya-ƙwaryar bikin da aka shirya babban ofishin bankin na ƙasa.