Wasu yara ‘yan biyu, Hassan Muhammad Nawad da Hussaini Muhammad Nawad da ke jihar Kano waɗanda shekarunsu 14, sun samar da wani abin girki mai amfani da fetur da ruwa wajen samar da wutar girki da ke shafe tsawon awanni biyar yana aiki.
Wannan abun girki yana da wani inji ne da ake sa masa batir, da kuma shi ne ke kaɗa ruwan da fetur ɗin wajen samar da wutar girgin.
Waɗannan yara dai, duk da kasancewar suna baban makarantar sakandare aji biyu (SS 2), amma sun samar da injin feshin ƙwari na lantarki da na ban ruwa.
A hirarsu da manema labarai, yaran sun ce daɗe suna so su yi amfani da ƙwaƙwalwarsu wajen samar da wani abu mai amfani ga al’umma.
A cewarsu, sukan tattauna ne a lokacin da suka zo kwanciya bacci kuma sun samu taimakon iyayensu da shawarwaru da sauransu.
Hassan ya ce sun fara tunanin yin abin girkin ne tun suna makarantar firamare.
Yace ba daɗe ina tunanin yadda aka yi gas ke iya ba da wutar da ake iya girki da ita.
Inda ya ce, yana da tabbacin wannan abu da suka samar zai taimaka wa al’umma, musamman la’akari da matsalar tattalin arziƙi da ake ciki.