Sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bar ƙasar nan zuwa wasu ƙasashen Turai domin hutu, inda daga can kuma zai zarce ƙasar Saudiyya domin aikin Umrah.
Kakakin zaɓaɓɓan shugaban ƙasar Tunde Rahman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
A cikin sanarwar kakakin ya ce, Tinubun ya fita ne domin ya je ya huce gajiyar yakin neman zabe da kuma harkokin zaben sannan kuma ya tsara shirinsa na karbar mulki kafin ranar kaddamarwarsa ta 29 ga watan Mayu na shekarar nan ta 2023.
Tunde ya ce zaɓaɓɓen shugaban ya nufi nahiyar Turai, inda zai je ƙasar Faransa da kuma London domin ya huta, sannan kuma ya wuce ƙasar Saudiyya domin ibadar Umrah da kuma azumin watan Ramadana.