Home » Sakacin Jami’an Mu Ne Ya Sa Bindigogi Ɓacewa- ‘Yan Sanda

Sakacin Jami’an Mu Ne Ya Sa Bindigogi Ɓacewa- ‘Yan Sanda

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Daga : Shareep Khaleepha Sharifai

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ɗora laifin ɓacewar bindigogi 3,907 a hannun jami’anta a kan sakaci da kuma ƙarancin iliminsu wurin kula da makamai.

Da take ƙarin bayani kan yawaitar ɓacewar bindigon, rundunar ta ɗora laifin ci gaban matsalar a kan abin da ta kira “sakacin” manyan jami’ai wajen tura ’yan sandan da ba su san ciwon kansu ba wajen aiki.

Rundunar ta bayyana takaicinta ne a wata takardar cikin gida daga “TERROR FOR ABUJA” wanda wakilinmu ya yi katarin samu a ranar Lahadi.

Takardar ta fito a yayin da Majalisar Dattawa take gudanar da bincike kan rahoton Babban Mai Binciken Kudi na Tarayya da ya nuna manyan bindigon ’yan sanda 3,907 sun ɓace.

Daga bisani kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fito ya bayyana cewa ɓata-gari ne suka yi awon gaba da bindigogin da ake magana a kai.

Ya kuma yi zargin cewa akwai aringizo a adadin da rahoton Babban Mai Binciken Kuɗin ya bayar na bindigogin da suka ɓace.

Sai dai kuma a wani saƙon cikin gida da Rundunar ta aika mai lamba CQ: 2400/DOPS/ CTU/FHQ/ABJ/VOL. 10/90, zuwa rassanta, ta gargaɗi manyan jami’anta cewa za su yaba wa aya zaƙi idan suka sake irin haka ta ƙara faruwa a ƙarƙashin jagorancinsu.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?