Home » A A Sule Ya Rushe Majalisar Zartarwarsa 

A A Sule Ya Rushe Majalisar Zartarwarsa 

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya rusa Majalisar Zartarwar Jihar tare da korar Sakataren Gwamnatin Jihar, Barista Muhammad Aliyu-Ubamdoma da kuma dukkanin hadimansa na musamman.

Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron gaggawa na musamman da aka gudanar a gidan gwamnati da ke garin Lafia babban birnin jihar a ranar Juma’a.

Jim kaɗan bayan tafiyar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shetima wanda ya kai ziyarar aiki ta kwana ɗaya a jihar domin ƙaddamar da wasu ayyuka a cikin jihar.

Wakilin Jaridar Aminiya ya ruwaito cewa, ana sa ran rushe hadiman Gwamnan zai yi tasiri sosai wajen gudanar da harkokin mulki da aiwatar da manufofin jihar.

Sai dai wani babban jami’in gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai cewa, duk da cewa har yanzu ba a bayyana dalilan da suka haddasa korar ma’aikatan gwamnatin ba, amma ya ce Gwamna Sule ya yi fice wajen yin garambawul ga tsarin tafiyar da harkokin gwamnatin jihar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?