Home » Sankarar Mama Na Barazana Ga Rayuwar Mata A Najeriya

Sankarar Mama Na Barazana Ga Rayuwar Mata A Najeriya

by Halima Djimrao
0 comment

Shugabar ƙungiyar ƙawararrun likitocin sankarar mama ta Najeriya ARCON, Nwamaka Lasebekon ta bayyana cewa Najeriya ta fi yawan matan da cutar ke kashewa a duniya.

Likitar ta faɗi haka ne a taron daƙile yaɗuwar cutar da aka yi a jihar Enugu. Nwamaka ta ce ya zama dole a ɗauki matakan yaƙi da yaɗuwar cutar musamman duba da yadda ta ke shafar tattalin arziki da rayuwar Bil Adama.

Dokta Nwamaka tace galibi cutar kan kama mata ne a lokacin da suke da ƙarfin yin aiki kuma suke kan haihuwa. Ta ce cutar ta fi kama mata kuma ana iya gadon ta, sannan rashin cin abinci mai gina jiki na iya haddasa cutar,  amma kuma shayar da jariri nono na iya samar da kariya ga mace daga kamuwa da cutar.

Nwamaka ta ce kamata ya yi mata su riƙa yin gwajin cutar lokaci-lokaci.  

Haka kuma  likitar ta ce akwai camfe-camfe da ake yi game da cutar saboda mata da dama da suka kamu da ita na danganta abun da jifa ko sihiri, maimakon su riƙa garzayawa asibiti sai su nufi bokaye da malaman tsubbu domin neman magani.

Ta ce ƙungiyar ARCON ta wayar da kan mutane kuma ta sanar da su hanyoyin samun kariya da yadda za a samu maganin cutar.

Nwamaka ta yi kira ga gwamnati,  da masu ruwa da tsaki da su samar da magungunan cutar a farashi mai sauƙi domin taimaka wa masu fama da cutar su iya samun magani.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi