• Home  
  • Kwamishinan ƴan sandan Kano CP Ibrahim Adamu Bakori ya yaba da yadda jarabawar ɗaukar aikin ƴan sanda ke gudana.
- Babban Labari

Kwamishinan ƴan sandan Kano CP Ibrahim Adamu Bakori ya yaba da yadda jarabawar ɗaukar aikin ƴan sanda ke gudana.

Kwamishinan ƴan sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana gamsuwarsa kan yadda masu neman shiga aikin ɗan sanda ke rubuta jarabawa cikin kwanciyar hankali a dukkan cibiyoyin da aka tanada. CP Bakori, ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarya ɗaya daga cikin cibiyoyin rubuta jarabawar domin duba yadda ake gudanar da […]

Kwamishinan ƴan sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana gamsuwarsa kan yadda masu neman shiga aikin ɗan sanda ke rubuta jarabawa cikin kwanciyar hankali a dukkan cibiyoyin da aka tanada.

CP Bakori, ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyarya ɗaya daga cikin cibiyoyin rubuta jarabawar domin duba yadda ake gudanar da ita da kuma yanayin tsaro don tabbatar da gaskiya.

Sanarwar ta fito ne ta bakin Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa.

Kwamishinan ƴn sandan, ya ce an tanadi jami’an tsaro don tabbatar da an kammala jarrabawar lafiya.

Ya kuma buƙaci masu rubuta jarrabawar, su bi ka’idojin da aka tsara, yana mai jaddada cewa shiga aikin ɗan sanda kyauta ne,kuma kar yadda da su bayar da kuɗi, domin duk wanda aka samu da laifin neman kuɗi zai fuskanci hukunci.

An jarrabawar a ranar Talata 28 ga watan Afrilu inda za a kammala ranar 30 ga watan Afrilun 2026

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000