Wasu mutum shida sun shiga hannun hukuma bisa zargin su da hannu a harin da aka kai a Kasuwar Wayoyi ta Farm Centre da ke Kano.
A ranar Litinin ne gungun masu ’yan daba ɗauke da makamai suka kai farmaki kasuwar a yayin da ake tsaka da hadahadar kasuwanci, inda suka riƙa yi wa ’yan wa ’yan kasuwar da masu wucewa fashin wayoyinsu da suarana kayayyaki.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan daban da suka faru wa kasuwar sun fito ne daga wurin wani taron siyasa a kusa da wurin.
Sanarwar da kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta ce mutum shida sun shiga hannu bayan jami’an rundunar sun kai ɗauki kasuwar tare da tarwatsa ɓata-garin, bayan samun kiran gaggawa da ke nuna cewa ’yan sanar na shirin zuwa faɗa a yankin Gyaɗi-Gyaɗi, inda kasuwar take.
Ya ce, “Da isar jami’an, sun iske ana wani ƙazamin tashin hankali, a yayin da ’yan dabar ke ƙoƙarin kai hari a wasu wurare.
“Sun kai wa jami’an tsaron hari da muggan makamai da duwatsu amma aka murƙushe su, inda daga nan suka tsere ta hanyar Kasuwar Farm Centre, inda suka yi ta ƙoƙarin fada shaguna da satar kayayyakin ciki.
“’Yan sanda sun sake bin su suka fatattake su, suka kama mutum shida. Yanzu al’amuran sun kafa a yankin,” in ji sanarwar da ya fitar.
Kiyawa ya kuma ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da jarumtaka da ƙwarewar jami’an Sashen Farm Centre da kuma waɗanda aka tura ƙarin taimako, yana mai cewa gaggawar daukar mataki ya hana taɓarɓarewar tsaro.
Ya yi gargaɗin cewa rundunar ba za ta lamunci ayyukan’yan daba ko duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya ba, tare da kira ga iyaye da masu kula da yara da su gargaɗi ’ya’yansu su guji shiga harkokin laifi.
Rundunar ta kuma ce ana ci gaba da bincike domin cafke waɗanda suka tsere tare da gano waɗanda suka ɗauki nauyin rikicin.
Haka zalika, an buƙaci mazauna yankin da su ci gaba da bai wa ’yan sanda sahihan bayanai domin taimakawa wajen kare rayuka da dukiyoyi a faɗin jihar
