Home » Sarakunan Jigawa Sun Taya Gwamna Namadi Murnar Samun Lambar Yabo

Sarakunan Jigawa Sun Taya Gwamna Namadi Murnar Samun Lambar Yabo

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi FCA, ya karbi bakuncin sarakunan jihar su biyar, wadanda uku daga cikinsu suka samu wakilcin hakimansu karkashin jagorancin shugaban majalissar sarakuunan jihar, Mai Martaba Alhaji Adamu Abubakar Make Haruna CON Sarkin Hadejia.

Ziyarar sarakunan na zuwa ne bayan dawowar gwamna Namadi Umar, daga bikin karbar lambar yabon da ya samu ta jaridar Leadership, kan iya shugabanci da aiyukan raya kasa wanda aka gudanar a dakin taro na Banquet Hall dake fadar shugaban kasa a birnin tarayya Abuja.

Haka zalika sarakunan sun yi masa barka da kamamala bukukuwan salla , kamar yadda aka saba bisa al’adun sarakuunan ga kowacce gwamnati bayan kammala bikin salla suke ziyartar gwamna.

Shugaban majalissar sarakuunan jihar, mai martaba Sarkin Hadejia, HRH Adamu Abubakar Maje CON , ya yabawa gwamnan jihar bisa kokarin da yake yi musamman wajen magance matsalolin tsaro da kuma kafa kwamiti na musamman kan kawo karhsen rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Sarakuunan sun kuma yabawa masa na shirya taron masalaha tare da cin abinci da manoma da makiyaya wanda akayi a kwanakin baya tare da jaddada godiyarsu bisa sanya hakimansu da sauran wakilansu cikin kwamitin gudanar da aikin gina sabbin cibiyoyin wankin Koda, a masarautun jihar guda 5 wadanda tuni aka fara gudanar da aikin don magance matsalolin ciwon koda a jihar Jigawa

Haka zalika mai martaba sarkin Hadejia , a madadin sarakunan jihar , ya yi kira ga al’umma su ci gaba da bawa gwamnatin Malam Umar Namadi goyon baya ¸ tare da yi masa addu’o’in samun nasarar aiwatar da muhimman aiyukan raya kasa daya sanya a gaba a fadin jihar.

Daya jawabi gwamna Umar Namadi , ya yabawa sarakunan bisa goyon bayan da suke bashi wajen aiwatar da aiyuka a fadin jihar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?