Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta kama mutane 8 cikin wadanda ake zargi sun fito fadan daba tare da jiwa Kansu raunuka, a unguwar kofar Na’isa ranar Alhamis din data gabata.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana a shafin sa na Facebook , ayau Asabar.
Rundunar yan sandan ta kuma bayyana damuwa, kan yadda matasan da suka samu raunukan, suka ki sanarwa da yan sanda, don kaisu asibiti a kula da lafiyarsu.
Kiyawa ya kara da cewa jami’an yan sanda sun shiga cikin unguwar, tare da mutane 8 da raunuka a jikinsu da kuma Wukake.
Sanarwar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike don kamo sauran wadanda ake zargi da aikata laifukan.
A ranar Alhamis din data gabata ne , wasu matasa da ake zargin Yan daba ne suka fito,Inda suka tayar da hankalin mazauna yankin da makotansu.