Mai Martaba Sarkin Bichi Alh Nasir Ado Bayero ya jagoranci bikin kaddamar da tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana, Wanda Kamfanin Sandstream Nigeria Limited da Hadi gwiwar majalisar masarautar Bichi suka samar a garin Yallami dake karamar Hukumar Bichi.
Sarkin ya nuna fari ciki bisa Samar da karamar tasha na wutar lantarki mai amfani da haske ranar tare da kira ga jama’a garin da su kula da kayan da aka Samar.
Sarkin ya kuma bayyana cewar karamar tasha zata taimaka wajen kara inganta hasken wutar lantarki a yankin, tare da Kara samar da kudaden shiga da aiyukan yi ga mata da matasa don inganta rayuwar al’ummar Masarautar.
Ya kuma yi alkawari Samar da abubuwan more rayuwa, ilimi da ayyukan yi ga jama’ar yankin
Shugaban Kamfani na Standstream Nigeria Limited Alh Ibrahim ya bayyana cewar Wutar za’a hadata da gidaje da kuma Shaguna dake garin na Yallami tare tabbacin cewar Kamfani hadi kai da Masarauta Bichi zai Samar da wutar lantarki ta hanyar Haske ranar ga Garuruwa da dama dake Karamar hukumar Bichi domin ingata kasuwanci da tatalin arzikin Jama’a.
A Jawabin Shugaban Karamar hukumar Bichi Ferfesa Yusuf Muhammad Sabo Wanda Sakataren Karamar hukumar Bichi Garba Usman ya wakilta, ya godewa Sarkin na Bichi tare da Kamfani bisa Samar da tasha wutar.