Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika, ya bayyana cewa, jirgin saman Najeriya zai fara aikinsa kafin ranar 29 ga watan Mayu 2023.
Hadi, ya sanar da hakan ne a taron masu ruwa da tsaki kan fannin sufurin jiragen sama karo na 10 da aka gudanar a babban birnin tarayya, Abuja.
A cewarsa, kararrakin kotu ne suka janyo cikas wajen fara aikin sabon jirgin saman.
Ya kuma ce an gayyato daukacin masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama masu zaman kansu don su zuba jarinsu a fannin amma suka ki saboda ba su aminta da aikin ba.
Sai dai, ya ce a yanzu ana ci gaba da tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayya da mahukuntan jirgin sama na Ethiopian Airlines, inda ya kara da cewa, a mataki na gaba majalisar zartarwar ta amince da yin hadakar.
A cewarsa, sabon jirgin zai taimaka matuka wajen kara bunkasa tattalin arzikin Nijeriya da yawon shakatawa da bude ido da samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar nan da kuma bunkasa fannin aikin noma. Da yake yin tsokaci kan kudaden da suka makale Hadi ya ce, gwamnatin tarayya ta dauki dukkan matakan da suka dace don ganin ba ta kara