Sarkin Dutse, Alhaji Muhammad Hamim Nuhu Sanusi, ya bayyana farin cikinsa game da samar da wata haɗaɗɗiyar rundunar Sojin runduna ta 26 da ake kira da Armoured Brigade a garin na Dutse tare da yi wa rundunar alƙawarin ba ta dukkan gudunmuwar da take buƙata.
Wannan kalamai na sarkin na zuwa ne a lokacin da Kwamanda na Farko na haɗaɗɗiyar rundunar Sojin ta 26, birgediya janar General Haruna Muhammad Abubakar, ya kawo wa sarkin ziyara.
Manufar ziyarar dai ita ce sanar da sarkin ayyukan da wannan haɗaɗɗiyar rundunar sojin za ta a garin na dutse da ma jihar bakiɗaya.
Sannnan kwamandan rundunar ya gode wa sarkin da ‘yan majalisar sarki bisa karrama su da aka yi tare da tabbatar da cewa wanzuwar wannan rundunar zai taimaka wajen daƙile duk wani yunƙuri na ayyukan ta’addanci a jihar da ma ƙasa bakiɗaya.
Haka kuma ya tabbatar wa da sarkin cewa Rundunar za ta yi aikinta cikin nuna ƙwarewa da dacewa da tanadin ƙundin tsarin mulki na ƙasa da na Gudanarwa Aikin Rundunar Sojin ƙasar nan.