Home » Sarkin Kano Na 15 Ya Haƙura Da Hawan Sallah

Sarkin Kano Na 15 Ya Haƙura Da Hawan Sallah

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
Yau Take Babbar Sallah

Daga Safiyanu Haruna Kutama

Mai Martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana janye gudanar da Hawan Sallah Ƙarama na wannan shekarar, yana mai bayyana cewa an dauki wannan mataki ne saboda dalilin tsaro da halin da Kano ke ciki a halin yanzu.

Sarkin ya sanar da wannan matsaya ne a yayin taron manema labarai da ya gudanar a daren ranar Laraba, inda ya yi kira ga al’ummar Kano da su yi hakuri da kuma bin doka da oda a wannan yanayi da aka tsinci kai.

Wannan mataki ya biyo bayan kokarin samar da kwanciyar hankali da kauce wa duk wani abu da ka iya kawo rudani a fadar masarautar.

Jama’a da dama sun karɓi wannan sanarwa da fatan alheri, tare da addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?